Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Tarayya, wato FAAC, ya raba Naira tiriliyan 2.225 a watan Agusta 2025, kuɗaɗen da aka ce sune mafi girma da aka taɓa rabawa tun samar da Najeriya.
Wannan shi ne karo na biyu a jere da rabon kuɗaɗe ya haura Naira tiriliyan 2, lamarin da ya samo asali daga ƙarin kuɗaɗen harajin mai da iskar gas, harajin kayayyakin cikin gida (VAT), da kuma kuɗaɗen da ake cirewa na CET.
Sanarwar da aka fitar bayan taron da aka gudanar a Abuja ta bayyana cewa daga cikin jimillar kuɗin, naira tiriliyan 1.478 sun fito daga kuɗaɗen haraji na yau da kullum, naira biliyan 672.9 daga harajin VAT, naira biliyan 32.3 daga kuɗaɗen da ake cirewa daga tura kuɗaɗe ta hanyar na’ura, yayin da naira biliyan 41.2 suka fito daga bambancin musayar kuɗi.
Daga cikin wannan rabo, gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 684.4, jihohi sun samu naira biliyan 347.1, yayin da ƙananan hukumomi suka karɓi naira biliyan 267.6.
Haka kuma, jihohin da ke samar da albarkatun ƙasa sun samu naira biliyan 179.3 bisa kashi 13% na kuɗaɗen da aka samu daga mai.
Wakilinmu ya tattaro cewa, daga kuɗaɗen harajin VAT, gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 100.9, jihohi suka karɓi naira biliyan 336.4, sannan ƙananan hukumomi suka samu naira biliyan 235.5.
Masana tattalin arziƙi sun bayyana wannan ƙarin rabo a matsayin alamar ƙaruwar kuɗaɗen shiga a zamanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa al’umma har yanzu na fama da tsadar rayuwa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook