Annobar amai da gudawa ta kashe mutane 58, ta kwantar da wasu da dama a Bauchi

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Aƙalla mutane 58 sun rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar sabuwar annobar cutar amai da gudawa da ta ɓulla a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 na Jihar Bauchi.

Bayanan da Daily Trust ta tattara daga ofishin gwamnatin jihar sun ce akwai sababbin mutane 258 da aka tabbatar da sun kamu da cutar.

Mataimakin gwamnan jihar, Malam Auwal Mohammed Jatau ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin yaƙi da amai da gudawa a matakin jiha da kuma kwamitin tsare-tsare na kula da cutar.

Ya ce, “Wannan ɓarkewa na cutar sau da dama ana iya kauce musu idan aka ɗau matakan gaggawa, daidaitattun matakai, da ci gaba a ɓangaren ruwa, tsafta da kula da muhalli (WASH). A halin yanzu Jihar Bauchi ta samu sababbin mutane 258 da suka kamu, tare da mutuwar wasu 58.”

Jatau ya ce duk da ƙoƙarin gwamnati, cutar cholera ta ci gaba da kasancewa babbar barazana ga lafiyar jama’a, inda ya bayyana cewa kafa kwamitocin ya zo a kan gaɓa wajen cimma nasarar da ake so.

Ya ƙara da cewa, “Kwamitin zai zama cibiyar tsara haɗin gwiwa domin jagorantar martanin ɓangarori da dama kan annobar amai da gudawa da kuma haɓaka tsare-tsaren kauce wa cutar a nan gaba tare da daidaita shi da shirin ƙasa na NCDC.”

Mataimakin gwamnan ya tunatar da ƴan kwamitin cewa, naɗin da aka yi musu shaida ce ta ƙwarewarsu da muhimmancin rawar da za su taka wajen tabbatar da sa-ido, gano cutar da wuri, da kuma mayar da martani cikin hanzari.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

BauchiLafiya
Comments (0)
Add Comment