Saƙon Godiya da Ban Gajiya ga Mahalarta Bikin Karɓar ƴan PDP zuwa APC a Birnin Kudu – Hon. Ado Maje (Retd.)

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Jigawa ta samu gagarumar nasara bayan mata 792 daga jam’iyyar adawa ta PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu.

Wakilinmu ya tattaro cewa dubban jama’a sun halarci wannan biki na sauya sheƙa, lamarin da masu shirya taron suka bayyana a matsayin tarihi ga jam’iyyar da al’ummar yankin.

Shugaban kwamitin shirya taron, Hon. Ado Maje Saleh (Rtd.), a madadin ofishin uwargidan Gwamnan Jigawa, Her Excellency Hajiya Amina Umar Namadi, ya miƙa saƙon godiya ga jama’ar da suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu wajen shaida wannan biki da waɗanda suka sauya sheƙar.

A cewarsa, His Excellency Gwamna Malam Umar Namadi ya tabbatar da ƙwarewa da kishin gaskiya wajen jan ragamar jam’iyyar APC a matsayin mafaka ta ci gaban al’umma, lamarin da ya sa jam’iyyar ke ci gaba da samun karɓuwa a faɗin jihar.

Ya ce, “Gwamnanmu yana aiki tuƙuru don tabbatar da ci gaban Jihar Jigawa a kowanne fanni. Mun gode masa, kuma muna tabbatar masa da goyon bayanmu a duk tafiyarsa ta siyasa,” in ji Hon. Ado.

Ya kuma godewa matar gwamna, Hajiya Amina Umar Namadi, bisa jajircewarta da nuna kulawa da kuma jagoranci na haɗa kan mata da matasa a jihar.

Kwamitin ya kuma godewa manyan jiga-jigan siyasa da suka halarci taron, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Bala Ibrahim; Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Bldr, Muhammad Uba; Shugaban APC na shiyya, Malam Yahaya Ahali Sakwaya; Shugaban APC na Birnin Kudu; shugabar mata ta APC a Birnin Kudu; matar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa; matar Sakataren Gwamnatin Jiha; matar Kwamishinan Harkokin Kasuwanci da Masana’antu; da kuma Dr. Hauwa Mustapha Babura, Ƙwararriyar Mai ba wa Gwamna Shawara kan Harkokin Ilimi.

Hon. Ado Maje ya kara jinjinawa mata da maza a matakai daban-daban da suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar taron.

Ya kuma yi kira ga sauran jama’ar jihar da ba su shiga APC ba da su yi tunani kan alfanun ci gaban al’umma ta hanyar mara wa jam’iyyar baya.

Ya ce, “Ƙofarmu a buɗe take ga duk mai kishin ci gaban Jigawa. Muna gayyatar kowa da kowa da ya shigo mu yi tafiya tare.”

Sauya sheƙar da aka samu ana kallonsa a matsayin ƙaruwar ƙarfi ga jam’iyya mai mulki a Jigawa, musamman a daidai lokacin da ake ci gaba da sa ido kan cigaban siyasar jihar.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

APCJigawaPDP
Comments (0)
Add Comment