Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Mutane goma sha tara sun rasa rayukansu a wani mummunan haɗari da ya auku a ƙauyen Gwalli, Ƙaramar Hukumar Gummi, Jihar Zamfara, lokacin da wata motar haya ta faɗa cikin rafi daga kan wata gada ginin gargajiya.
Rahotannin da wakilin Daily Trust ya tattara daga mazauna yankin sun nuna cewa, mutanen da ke cikin motar sun nufi ƙauyen Sakaba na karamar hukumar Wasagu, Jihar Kebbi ne daga Jihar Zamfara, domin raka sabuwar amarya zuwa gidan mijinta.
Motar Toyota Hummer da aka ce za ta iya ɗaukar fasinjoji 18, ta ɗauki sama da mutum 40 kafin ta kife cikin rafin.
An gano cewa aƙalla mutane 21, ciki har da amaryar da direban motar, sun tsira daga haɗarin.
Wata da ta shaida faruwar haɗarin, Rabi, ta bayyana yadda abokiyarta ta tilasta mata sauƙa daga cikin motar kafin haɗarin ya faru.
Ta ce, “Da ba ta tilasta min na sauƙa daga motar ba, da yanzu ni ma ina cikin waɗanda suka mutu. Mun shaida lokacin da motar ta nutse cikin ruwan tare da fasinjojin da ke cikinta. An sami gawar wata mace rungume da ɗanta, dukkansu a mace.”
Liman Bello Muhammad Gwalli, wani shaidar gani da ido, ya bayyana cewa motar ta yi ƙoƙarin ƙetare rafin bayan wata mota ta farko ta riga ta wuce lafiya.
Amma motar ta tsaya cak, direban ya sauƙa domin bincike, sannan ya buƙaci wasu daga cikin matan su sauƙa.
Suna sauƙa kuma, motar ta karkace ta faɗa cikin rafin.
Wani dattijo a yankin, Alhaji Shehu Gumi, ya bayyana cewa direban ya yi yunƙurin kauce wa wani ƙarfen gada da ya fito fili, lamarin da ya haifar da rashin daidaito kafin fasinjojin su sauƙa.
“Ƴar abokin nawa da ɗanta sun tsira, amma ɗan matar kishiyarta na cikin waɗanda suka mutu,” in ji shi.
Hon. Adamu Gumi, Ɗan Majalisar Wakilai da ke wakiltar yankin, ya bayyana ɓacin rai kan yadda aka yi watsi da hanyoyin yankin tsawon shekaru.
“Na gabatar da kudiri a majalisa, kuma an saka a kasafin kuɗi, amma ba a aiwatar da komai ba. Wannan sakaci ne ya haddasa mutuwar mutane 19,” in ji shi.
Kakakin rundunar ƴan sanda na Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya danganta shi da cunkoson fasinjoji a motar.
Ya gargaɗi direbobi da su guji yin lodin da ya wuce ƙarfin abin hawa domin kare rayuka.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook