An kama wani tsoho ɗan shekara 70 da zargin lalata da ƙananan yara ta hanyar yaudararsu da kuɗi a Bauchi

Rundunar ƴan sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa, jami’anta sun kama wani dattijo mai shekaru 70, Lawan Sani, bisa zargin yin lalata da wasu ƴan mata uku bayan ya yaudare su da kudi ₦500.

Rahoton ya bayyana cewa wanda ake zargin, wanda ke aiki a matsayin mai gadi a unguwar Sarakuna, ya riƙa amfani da kuɗi wajen jawo ƙananan yara mata zuwa gidansa kafin ya yi lalata da su tare da yin barazanar hana su faɗawa wani.

An kama shi ne bayan wani yunƙuri da bai yi nasara ba a kan wata yarinya mai shekaru 16, a ranar 1 ga Satumba, 2025, inda aka cafke shi a wurin da lamarin ya faru.

Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar, Ahmed Wakil, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata.

Ya ce, “Da samun rahoton, jami’an da ke ƙarƙashin C Divisional Police Headquarters, ƙarƙashin jagorancin DPO SP Naziru Abubakar Pindiga, suka yi gaggawa suka kama wanda ake zargi.

“A yayin bincike, ya amsa cewa ya taɓa jawo wata ƙarama da ₦500 zuwa wannan gida domin ya yi lalata da ita.”

Wakil ya ƙara da cewa binciken ya gano cewa Sani ya riga ya yi wa wasu ƴan mata biyu irin wannan ɓarna ta hanya iri ɗaya.

“Haka kuma, an kira waɗanda abin ya shafa zuwa wurin bincike, inda suka tabbatar da zargin tare da bayyana cewa wanda ake zargi ya yi lalata da su fiye da sau 15 a lokuta daban-daban, tare da yi musu barazana kada su shaida wa kowa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa an kai waɗanda abin ya shafa asibiti domin a duba lafiyarsu.

Wakil ya yi amfani da damar don jaddada aniyar rundunar ƴan sanda na yaƙi da laifuka a jihar, “Magance ƙalubalen tsaro na zamani yana buƙatar ƙara ƙarfin aikin ƴan sanda ta hanyar sabbin kayan aiki da ingantattun hanyoyi. Wannan shiri na nufin yaƙi da ƙaruwa da laifukan da ke barazana ga al’ummarmu. Duk da ƙalubalen da ke tattare da wannan aiki, muna nan tsaye kan nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mana wajen kare kowa.”

Sanarwar ta ƙara da cewa kwamishinan ƴan sanda na Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya yi kira ga jama’a da shugabannin al’umma su tallafa wa rundunar ƴan sanda, “Muna kira ga haɗin kai da goyon baya ga rundunar ƴan sandan Najeriya daga kowane ɓangare, yayin da muke aiki tare domin samar da muhalli da ƴan ƙasa za su rayu cikin kwanciyar hankali da tsaro.”

Kama Sani na daga cikin yunƙurin tsaurara matakai kan lalata yara da rundunar ƴan sanda ke yi, wanda ya kai ga kama mutane fiye da 70 cikin ƙasa da watanni shida.

In za a iya tunawa, a irin wannan lamari a watan Agusta, an kama maza biyar bisa zargin yin lalata da wata yarinya mai shekaru 10 a ƙauyen Zadawa, da ke Ƙaramar Hukumar Misau ta Jihar Bauchi.

Bauchi
Comments (0)
Add Comment