Amaechi ya ce, Tinubu “Ba shi da wayo, an kayar da shi a Legas”, ya buƙaci haɗin gwiwa don kayar da shi a 2027

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma babban jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya buƙaci ƴan Najeriya da su shirya yin zaɓe mai tarin jama’a a 2027 domin hana Shugaba Bola Tinubu samun wa’adi na biyu.

TIMES HAUSA ta tattaro daga taron cika shekaru biyar na First Daily, wanda ya gudana a Abuja, cewa Amaechi, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a Agustan da ya gabata ya ce, nasarar da Tinubu ya rasa a Legas a 2023 hujja ce cewa ba shi da “ƙarfin da zai hana a iya kayar da shi”.

Amaechi ya ce, “Idan kana cewa an riga an rubuta sakamakon, hakan yana ƙara yawan rashin fitowar masu jefa ƙuri’a. Rashin fitowar ne zai dawo da Tinubu Villa. Mutane su tashi su fito su kaɗa ƙuri’a.”

Ya ƙara da cewa, “Idan Tinubu wanda ba zai kayu ba ne ‘invincible’, ta yaya aka kayar da shi a Legas? Za a iya maimaita hakan. Amma dole mu yarda cewa ba shi da wani tsafi.”

Amaechi ya yi zargin cewa gwamnati mai ci ba ta da ikon yin sahihin gyaran zaɓe, yana mai cewa, “Babu wata gwamnati mai ci da za ta yi gyaran zaɓe. Mun gwada, mun faɗi.”

Ya kuma zargi jam’iyyun adawa da rashin tsari da gazawar tsara makaman karawa da gwamnati.

“Jam’iyyun adawa su ne matsala. Ba sa tattauna yadda za a ceci Najeriya; ba sa ma tattauna yadda za a canza ɗan takara.”

“Magudin zaɓe shi ne mummunan juyin mulki” – tsohon gwamnan Bayelsa

TIMES HAUSA ta tattaro cewa tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana maguɗin zaɓe a matsayin “mummunan juyin mulki” da ke ƙwace ikon jama’a.

Ya ce, “Sace sakamakon zaɓe shi ne mafi muni cikin take haƙƙin jama’a. Mutane ba sa zaɓe, amma ana rubuta sakamakon sannan a ce su tafi kotu. Wannan juyin mulki ne.”

Dickson ya ce ya sha ganin irin waɗannan abubuwa a lokacin da yake gwamna a jam’iyyar adawa.

Sam Amadi ya caccaki tsarin INEC da siyasar kuɗi

A jawabin sa, Daraktan Abuja School of Social and Political Thought, Dr. Sam Amadi, ya yi suka ga tsarin zaɓe na Najeriya, yana mai cewa mutanen da ke kula da zaɓuka duk suna da alaƙa da shugabannin siyasa.

Ya ce, “Mun daina naɗa mutane masu zaman kansu domin kula da zaɓe. Zaɓukanmu kullum akwai maguɗi. Tsadar kamfen da ribar ofis sun mayar da zaɓe tamkar yaƙi.”

Ya buƙaci a jama’a su tsananta matsi ga INEC da masu ruwa da tsaki.

Sauran jawabai

Mai wallafa First Daily, Daniel Markson, ya yi nadamar cewa, “A gaskiya, Najeriya ba ta taɓa yi min aiki ba. Muna da matsalar shugabanci. Mun ci amanar kanmu.”

Ya sanar da shirin wayar da kai kan zaɓe a faɗin ƙasa a shekarar mai zuwa.

Taron ya tattauna irin ƙalubalen rashin sahihin zaɓe, batun maguɗin sakamako, da tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya tafi bisa amana da gaskiya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

AmaechiTinubu
Comments (0)
Add Comment