Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da tsoratarwa da tayar da hankali bayan harin da aka kai wurin taronta a wani coci a Alimosho, Jihar Lagos.
Wakilinmu, Faruk Ahmad, ya tattaro daga wata sanarwa da mai magana da yawun ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya wallafa a dandalin X a ranar Lahadi, yana cewa, “APC na jin tsoron shaharar ADC a faɗin ƙasa, kuma matakin da suka iya ɗauka shi ne na tayar da hankali da tsoratarwa.”
Ya ƙara da cewa: “Harin da aka kai jiya a coci inda ake gudanar da taron ADC a Alimosho sabon tabo ne, yana mai nuna cewa APC ba ta daraja ko da Coci ba.”
Jam’iyyar ta kuma zargi APC da amfani da ƴan sanda a matsayin rundunar Gestapo na jam’iyya mai mulki ta APC, abin da ta ce na haifar da barazana ga dimokuraɗiyya da ƴancin siyasa a ƙasar.