Abin da ya faru da Shugaban NMDPRA Farouk Ahmed har ta sa yai murabus

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Farouk Ahmed ya yi murabus daga muƙaminsa na Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur da Kasuwancinsa ta Ƙasa (NMDPRA), a daidai lokacin da ake ci gaba da zarginsa da cin hanci da rashawa daga Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya kuma tabbatar da cewa Gbenga Komolafe ya bar muƙaminsa na Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur a Tsandauri (NUPRC).

Onanuga ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen wasu sababbin mutane biyu zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa da su a matsayin masu maye guraben da aka samu.

A cewar sanarwar, Shugaban Ƙasa ya nemi Majalisar Dattawa da ta gaggauta tabbatar da Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin Shugabar NUPRC, yayin da Saidu Mohammed aka zaba a matsayin sabon Shugaban NMDPRA.

“Dukkanin mutanen biyu ƙwararru ne kuma gogaggu a fannin man fetur da iskar gas,” in ji sanarwar a wani ɓangare.

TIMES HAUSA ta fahimci cewa sa’o’i kadan kafin murabus ɗinsa, Ahmed ya kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

An gan shi sanye da shigar kayan gargajiya, kuma bai wuce mintuna 30 ba kafin ya bar fadar shugaban ƙasa.

Dalilin ziyarar bai fito fili ba, sai dai ya ƙi yin magana da manema labarai, inda ya ce, “Lokaci ya ƙure domin yin hira. Ƙarfe biyar ta wuce, lokacin aiki ya wuce.”

Zargin Dangote da Neman Adalci

Ziyarar tasa ta zo ne a daidai lokacin da rikici ya ɓarke tsakaninsa da Dangote, lamarin da ya sa attajirin ya kai ƙara Hukumar ICPC, yana zargin Ahmed da cin hanci da almundahana.

Dangote, ta hannun lauyansa Ogwu Onoja, ya buƙaci hukumar ICPC da ta kama, da bincika tare da gurfanar da Ahmed a gaban kotu.

Dangote ya zargi Ahmed da rayuwa sama da samunsa, inda ya yi iƙirarin cewa ƴaƴansa huɗu sun yi karatun sakandare a Switzerland da kuɗin da ya kai miliyoyin daloli.

Ya ce kusan dala miliyan biyar aka kashe wajen karatun sakandare da kula da su tsawon shekaru shida, sannan wasu ƙarin dala miliyan biyu a manyan makarantu, ciki har da zargin biyan dala 210,000 domin shirin karatun MBA na shekarar 2025 a Jami’ar Harvard ga ɗaya daga cikin ƴaƴan Ahmed.

Dangote ya lissafa sunayen yaran da makarantun da suke karatu, yana mai roƙon ICPC da ta gurfanar da Ahmed bisa dokokin ƙasa.

“Ba mu da wata shakka cewa tunda al’amarin ya shahara a bainar jama’a, hukumar ba za ta rufe ido ba, sai ta ɗauki matakin da ya dace domin tabbatar da adalci da kare martabar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” in ji wani ɓangare na ƙarar.

ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafin, tana mai alƙawarin cewa za a “yi cikakken bincike” a kai.

Zargin Zagon Ƙasa ga Tattalin Arziƙi da Martanin Ahmed

A ranar Lahadi, Dangote ya ƙara zargin shugabancin NMDPRA ƙarƙashin Ahmed da aikata “zagon ƙasa ga tattalin arziƙi,” yana mai cewa, wasu matakan hukumar na raunana matatun mai na cikin gida.

A wani taron manema labarai a Matatar Dangote da ke Legas, ya zargi hukumar da ci gaba da bayar da lasisin shigo da man fetur, wanda ke daƙile ayyukan matatun cikin gida tare da ƙara dogaro da shigo da kaya daga waje.

Ya ce akwai haɗin baki tsakanin hukumar da ƴan kasuwar man ƙasa da ƙasa da masu shigo da mai, wanda ke cutar da ƴan kasuwar gida.

Sai dai Ahmed, a wata gajeriyar sanarwa, ya bayyana waɗannan zarge-zarge a matsayin “marasa tushe kuma ƙirƙirarru.”

“Duk da cewa na san irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe da aka yi min ni da iyalina, a matsayina na mai kula da muhimmin ɓangare, na zaɓi kada in shiga hayaniyar jama’a,” in ji shi.

“Yanzu da aka kai batun gaban hukuma mai bincike, ina da yaƙinin hakan zai ba da damar tantance gaskiya cikin adalci da kuma wanke sunana,” in ji Ahmed.

Rikici Mai Tsawo da Shiga Tsakanin Majalisa

TIMES HAUSA ta fahimci cewa rikicin Dangote da Ahmed ya samo asali ne tun shekarar 2024, lokacin da NMDPRA ta zargi matatun mai na cikin gida, ciki har da Dangote Refinery, da samar da kayayyaki marasa inganci idan aka kwatanta da na waje.

Ahmed ya taɓa zargin Dangote da yunƙurin mallake kasuwar makamashi gaba ɗaya, zargin da matatar ta musanta.

Haka kuma hukumar ta ce matatar Dangote na cikin matakin gwaji ne kawai kuma ba ta da cikakken lasisin yin aiki daga gwamnati.

Wannan ya sa Majalisar Wakilai ta kira da a gudanar da bincike tare da dakatar da Ahmed a wancan lokacin.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

NMDPRATinubu
Comments (0)
Add Comment