Ɗan Majalissar Jiha, Rossy, ya yi kira ga al’ummar Birnin Kudu da su yi rijistar zaɓe

Ɗan majalisar Jihar Jigawa mai wakiltar mazaɓar Birnin Kudu, Honourable Muhd Kabir Ibrahim Yayannan Rossy, ya yi kira ga al’ummar mazaɓarsa da su yi amfani da damar rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) da ke gudana a halin yanzu domin tabbatar da ƴancinsu na zaɓe.

A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, Hon. Yayannan Rossy ya bayyana cewa samun katin zaɓe ba kawai wajibi ba ne don yin zaɓe, amma shaida ce ta ƴancin shiga tsarin demokaraɗiyya, makullin zaɓen shugabanni da kuma makamin yin hisabi ga shugabanni a duk matakan mulki.

“Ba tare da sahihin katin zaɓe ba, muryarku ba za tai ƙara ba lokacin da ake yanke muhimman hukunci kan al’amuran da za su tsara makomar mazaɓarmu, jiha da ƙasar mu,” in ji shi.

Ya yi kira ga iyaye da su jagoranci ƴaƴansu da suka kai shekarun ƙa’idar kaɗa ƙuri’a, malamai su yi faɗakar da ɗalibai, malaman addini su yi kira a kan minbarin huɗuba, shugabannin gargajiya su motsa al’umma, ƙungiyoyin matasa da mata, ƴan kasuwa da sauran ƙungiyoyin fararen hula su yaɗa wannan saƙo.

“Mu tabbatar cewa kowanne ɗan mazaɓarmu da ya cancanta ya yi rijista, ya samu ƙarfin iko, kuma ya shirya yin zaɓe cikin ƴanci a zaɓuɓɓukan da ke tafe,” in ji shi.

Hon. Yayannan Rossy ya ƙara jaddada cewa nagartaccen mulki yana farawa ne daga ingantaccen zaɓe, kuma ingantaccen zaɓe yana yiwuwa ne ga waɗanda suke da ikon kaɗa ƙuri’a. “Makomar Birnin Kudu za ta dogara da ƙarfin jama’armu a akwatin zaɓe – kuma hakan yana farawa ne da yin rajista yau. Mu yi aiki tun yanzu, don kanmu, iyalanmu, da zuri’armu masu zuwa,” in ji shi.

Birnin KuduCVR
Comments (0)
Add Comment