Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Daga: Ahmed Ilallah
A wani taro ranar Alhamis da Shugaba Tinubu ya yi da Gwamnonin Jama’iyar APC ya yi kira gare su da su aiwatar da umarnin Kotun Ƙoli na ba wa ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu.
Wannan batu kamar almara, shin Gwamnatin Tarayya ce mai aiwatar da hukuncin ko kuma jihohin da aka yi hukuncin a kansu?
Ragnar 11 ga watan 7 na shekara 2024, kimanin shekara guda da rabi kenan da Kotu Ƙoli ta yanke hukuncin ba wa ƙananan hukumomin Najeriya ƴancin cin gashin kansu na ba da umarnin turawa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye ba tare da haɗaka da jahohinsu ba.
Gwamnatin Tinubu ce ta kai ƙarar gaban wannan kotu, wanda a ke ganin ƙarar da gwamnatin ta kai don samun wannan hukuncin a cike take da siyasa.
Amma har yanzu wannan hukuncin ya gagara aiwatarwa a mulkin na Shugaba Tinubu.
Gashi dai Shugaban ya tuƙa amalarsa yadda ya ke so, amma ya gagara yin loma.
In zamu iya tuna baya, a lokacin da Shugaba Tinubu yake mulkin Jihar Legas, ya samu tangarɗa da Gwamnatin Shugaba Obasanjo a kan ƴancin ƙananan hukumomi, har ta kai an riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin Jihar Legas.
Amma da suka kai ƙara wannan kotun ta ƙoli, a ka tilastawa Gwamnatin Shugaba Obasanjo ba su kuɗaɗensu.
Shin me ya kasa aiwatar da wannan hukuncin?
Ƴancin ƙananan hukumomi an maida shi wani faɗa na siyasa tsakanin gwamnatin sama da ta tsakiya, don neman tagomashi da ikon mallaka.
Gwamnonin suna son su yi chaka da ƙananan hukumomi, shi kuma shugaban ƙasa na son ya yi mali da su.
Kamar yadda na faɗa a baya, Shugaba Tinubu lokacin yana gwamna bai yarda ba, amma yanzu da ya zama shugaban ƙasa, ya ke son aiwatarwa.
Amma, a zahirin gaskiya duk wanda ya yi nazarin tanade tanaden da Kudin Tsarin Mulkin Nijeriya Na 1999 ya yi a kan ƙananan hukumomi ya san, dole sai an yi gyararraki, kafin a ce ƙananan hukumomi sun sami cikakken ƴanci.
Har yanzu babu wata ingantacciyar demokaraɗiyya wajen gudanar da ƙananan hukumomi a Najeriya, kama daga zaɓe mai inganci, gudanar da mulkinsu, da ma tsarin aiwatar da aiyukansu.
Hakazalika, dalilin siyasar da ta sanya neman wannan hukuncin, kuma siyasa tana neman hana aiwatar da hukuncin, ya kamata ana cizawa ana hurawa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook