Ƴan Tinubu na ƙalubalantar kiran yin bore irin na Nepal a Najeriya yayin da wasu ke cewa in ba ai gyaraba akwai matsala

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Wasu magoya bayan Shugaba Bola Tinubu sun soki kiran da ake yi a shafukan sada zumunta na yin zanga-zanga a Najeriya, bayan tarzomar da matasan Nepal suka gudanar wadda ta kifar da Firayim Minista na ƙasar.

Wannan kira na zuwa ne bayan gagarumar zanga-zanga a Nepal inda matasa suka yi bore kan irin jin daɗin da shugabanni ke yi, suka ƙona manyan gine-ginen gwamnati ciki har da majalisa da kotun ƙoli.

A Najeriya, wasu masu amfani da dandalin X sun yi kira da matasa su yi koyi da Nepal.

Juwon Sanyaolu na ƙungiyar Take-It-Back Movement ya rubuta cewa, “Amurka ta yi Black Lives Matter a 2020, mu muka yi #EndSARS. Kenya ta yi bore kan ƙudirin kasafin kuɗi a 2024, mu muka yi #EndBadGovernance. Yanzu Nepal ta yi nasu. Shin 2025 matasan Najeriya za su yi nasu kuwa?”

Sai dai magoya bayan gwamnati sun yi gargaɗi cewa duk wani yunƙurin yin bore zai iya zama mafi muni fiye da na #EndSARS a Najeriya.

Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara, Reno Omokri, ya yi gargaɗin cewa, “Muna ƙin abin da ya faru a Nepal. Najeriya ba za ta amfana da tarzoma irin wannan ba.”

Haka shi ma shahararren ɗan wasan barkwanci Seyi Law ya bayyana cewa waɗanda ke goyon bayan tarzoma ba sa gane cewa hakan zai shafi talakawa fiye da shugabanni ba.

Ƙungiyoyin farar hula kamar Rivers Civil Society Organisations da Committee for the Defence of Human Rights sun yi tsokaci kan lamarin, inda suka jaddada cewa matsin tattalin arziƙi a Najeriya na iya haifar da irin wannan bore idan gwamnati ba ta gyara ba.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

BoreNajeriyaZanga-Zanga
Comments (0)
Add Comment