Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta ce ta samu nasarar daƙile satar shanu da kuma kama waɗanda suka lalata wayoyin wutar lantarki a wasu sassan jihar, tare da kama mutane da dama da ake zargi da hannu a cikin laifukan.
Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar da kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ya fitar cewa, an yi nasarar ne a ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴan sanda, CP Dahiru Muhammad, ta hanyar haɗa kai da al’umma da kuma amfani da bayanan sirri.
A cikin rahoton, an ce a ranar 27 ga Agusta 2025 da misalin ƙarfe biyu na dare, wani Usman Yusuf mai shekara 25 daga Boguwa Fulani a Malam Madori tare da wani abokinsa Haruna Birau (wanda ya tsere), sun kutsa gidan wani Alhaji Adamu Hussaini a Maidaru, inda suka saci jan sa guda ɗaya da kuɗinsa ya kai Naira dubu ɗari takwas.
An samu nasarar ƙwato dabbar daga hannun Usman, yayin da ake ci gaba da neman abokin nasa.
Haka zalika, a ranar 30 ga Agusta, jami’an sashen “B” na Hadejia sun cafke wasu mutane biyu – Isubu Adamu, wanda ake kira Banbalasta, da kuma Danladi Maikudi – suna tuka mota ɗauke da shanu biyu da aka sato.
Isubu ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa sun yi satar ne tare da wani Datti daga Guri, wanda ya tsere.
Kazalika, a ranar 2 ga Satumba, jami’an ƴan sanda daga Auyo sun kama wani Umaru Audu daga Kuhurdu Fulani a Malam Madori, ɗauke da shanu biyu da aka sace daga gidan Maijama’a Sule a Kaugama.
A ranar da ta biyo baya kuma, aka kama wani Ali Alhaji Buji mai shekara 25 da shanu biyu daga cikin shanu huɗu da tumaki tara da aka sace daga hannun wani Hassan Zkitu a Taura.
Bugu da ƙari, jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai shekara 23 mai suna Amadu Muhammad daga Guri, ɗauke da wayoyin wutar lantarki da aka sata, waɗanda aka ɓoye a cikin buhunan takin zamani a Margadu, yayin da yake ƙoƙarin kai su Nguru a Jihar Yobe, sai da abokin laifinsa ya tsere.
Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’an da kuma ƴan sa-kai (Ƴan bulala) bisa jajircewarsu.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanan sirri da wuri domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.