Ƴan Sanda sun ritsa gungun ɓarayin kayan lantarki da ke jefa ƴan Jigawa cikin duhu

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta rusa wata babbar ƙungiyar masu lalata kayayyakin lantarki da ake zargin sun lalata transfomomi 15 da manyan wayoyin wuta waɗanda darajarsu ta kai miliyoyin nairori a sassa daban-daban na jihar.

Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar a ranar Asabar cewa jami’an ƴan sanda daga sashen ‘B’ na Hadejia, bayan samun rahoto, sun kama mutum takwas a unguwar Matsaro ta Ƙaramar Hukumar Hadejia, a ranar 18 ga Agusta, 2025.

Masu laifin sun haɗa da Haruna Musa (36), Hussaini Innocent (23), Abubakar Yakubu (27), Zakariyya Mohammed (20), Mamman Danladi (27), Khalifa Yahaya (18), Ibrahim Mohammed (20), da Ali Ibrahim (20) – waɗanda ake zargi sun yi haɗin baki a lokuta da dama wajen lalata transforma a Auyaka, Gandun Sarki, Shagari, Jama’are, Agumau, Gawon Dogari, Tsohuwar Tasha, da Unguwar Matsaro a Hadejia, da kuma Jabo a Kafin Hausa da Yamide a Auyo.

Haka kuma, an cafke wasu mutane biyu, Idris Nuhu (35) da Abdullahi Idris (22), mazauna Makara Huta, Hadejia, bisa zargin siyan sassan transfomomin da aka sata kan naira 380,000, inda rahotanni suka tabbatar an kai wasu Kano inda aka sayar da su kan naira 680,000.

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da bincike don kama sauran da suka gudu, yayin da tuni aka gurfanar da waɗanda aka kama a kotu.

A wani lamari daban kuma, an kama wasu mutane biyu, Sani Sa’idu (25) ɗan Bamaina a Birnin Kudu, Jihar Jigawa da abokinsa Isah Isyaku (25) ɗan Kano, ranar 2 ga Satumba, 2025 bisa zargin lalata manyan wayoyin wutar lantarki masu sulke da darajarsu ta kai naira miliyan 7 tare da satar kwamfutar tafi-da-gidanka, wayar Vivo da kuma kuɗi naira 20,000 daga gidan ma’aikacin Academy of Gifted, Bamaina.

Rundunar ƴan sandan ta ce an ƙona wayar lantarkin a ajin makarantar sakandare domin cire ƙarfen da ke cikinta.

An ƙwato kayan da aka sace, yayin da ake ci gaba da bincike kan wanda aka ce ya karɓi kayan a Kano.

Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya jaddada cewa ba za a bar ɓarayin kayayyakin gwamnati su ci gaba da yawo ba a jihar.

Ya ce, “Ba inda laifi zai ɓuya a wannan jiha. Duk wanda aka samu da laifi za a kama shi, a bincike shi, a gurfanar da shi,” yana mai roƙon jama’a da su riƙa hanzarta kai rahoton lalacewar kayayyaki domin a ɗauki mataki a kan lokaci.

Jigawa
Comments (0)
Add Comment