Jami’an ƴan sanda a jihar Jigawa sun samu nasarar cafke mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da ƴan fashi, ɓarayin babura, da masu satar wayoyi, inda suka ƙwato babura uku, wayoyin hannu biyu da wuƙa daga hannun su.
Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar da Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam, cewa rundunar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴan Sanda, CP Dahiru Muhammad, na ci gaba da kai hare-hare na musamman kan masu laifi domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
An bayyana cewa, daga cikin nasarorin da aka samu sun haɗa da cafke Yunusa Usman, mai shekara 22, a Hadejia bayan ya sace wayoyin Huawei da Redmi tare da caccaka wa wani mutum wuƙa.
Haka kuma, an cafke mutane biyu a Dutse yayin da suke ƙoƙarin sace babur, waɗanda daga baya suka amsa laifin.
Sauran nasarorin sun haɗa da kama ɓarayin wayoyi biyu a Takur Site, cafke wani mai suna Musa Bala a Roni da babur da ya sato, da kuma cafke wasu mutum biyu a Dutse da ke ƙoƙarin tserewa da babur Hyungen zuwa Kano.
Kwamishinan Ƴan Sandan ya yaba wa jami’ansa bisa ƙwazon da suka yi, yana mai kiran jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai da kuma sanar da duk wani motsi mai haɗari ga ofishin ƴan sanda mafi kusa.
“Za mu gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike,” in ji shi.