Ƴan sanda sun ƙaryata tallata ɗaukar sabbin ma’aikata da ke yawo a kafofin sadarwa

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rundunar Ƴan Sandan Najeriya ta ƙaryata wata sanarwa da ta yaɗu a shafukan sada zumunta wadda ke iƙirarin cewa za a buɗe sabuwar damar ɗaukar sabbin ma’aikata daga ranar 22 ga Satumba, 2025.

Sanarwar bogi mai taken “Nigeria Police Force Recruitment Exercise 2025” ta nemi ɗaliban da suka kammala SSCE, OND, HND da B.Sc. su nemi aikin, tare da gabatar da jerin sharuɗɗa da hanyoyin neman.

Rundunar ƴan sanda ta bayyana sanarwar a matsayin ta ƙarya da kuma yaudara ga jama’a.

Wakilinmu ya tattaro daga wata wallafa da rundunar ta yi a shafinta na X a ranar Alhamis cewa an saka alamar “FAKE” a saman takardar don nuna cewa ba ta fito daga hannun hukumar ba.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su yi hattara da masu amfani da irin waɗannan shafukan domin cutarwa.

Sanarwar bogin ta yi iƙirarin cewa masu neman aikin dole su kasance ƴan Najeriya ta hanyar haihuwa tare da shaidar NIN mai inganci.

Haka kuma ta kafa iyaka na shekaru tsakanin 18 zuwa 25 ga masu SSCE da OND, da kuma shekara 28 ga masu HND da B.Sc.

Ta kuma buƙaci tsayin mita 1.67 ga ma’aikata maza da mita 1.64 ga mata, tare da samun aƙalla sakamako mai kyau a darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Baya ga haka, sanarwar ta buƙaci masu neman aikin da su gabatar da takardun haihuwa, shaidar asali, da takardar garanto, sannan su cike fom ɗin yanar gizo da takardun karatu.

Sai dai, wakilinmu ya tattaro daga rahoton da jaridar PUNCH Online ta buga cewa Hukumar Kula da Ayyukan Ƴan Sanda (PSC) ta riga ta gargaɗi al’umma a ranar 30 ga Agusta cewa duk wani talle da ake yaɗawa kan ɗaukar ma’aikata a shekarar 2025 ba na gaskiya ba ne.

Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana a cikin sanarwar cewa babu wani shiri da aka ƙaddamar na ɗaukar ma’aikata a yanzu, yana mai jaddada cewa hukumar ba ta taɓa amfani da irin waɗannan hanyoyin sadarwa wajen bayar da sanarwa ba.

Ani ya ƙara da cewa an sha gargaɗin matasa masu son shiga aikin ɗan sanda da su kasance masu haƙuri, su jira sahihiyar sanarwar da hukumar za ta bayar a hukumance kan ɗaukar ma’aikata.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Daukar Ma'aikatayan sanda
Comments (0)
Add Comment