Ƴan bindiga sun kashe mutum takwas, sun kuma ƙone motocin sintiri biyu tare da yin garkuwa da mutane uku a wani hari da suka kai ƙauyen Magaji Wando a Ƙaramar Hukumar Dandume, Jihar Katsina.
Wakilinmu Bashar Aminu ya tattaro daga tattaunawar da aka yi da mazauna yankin cewa, harin ya fara ne a daren ranar Juma’a ya kuma ci gaba har safiyar Asabar, inda ƴan bindigar suka shiga ƙauyen suna harbi ba ƙaƙƙautawa.
“Mutum biyar sun mutu nan take, biyu kuma sun rasu daga raunin harbin bindiga daga baya,” in ji wani mazaunin ƙauyen.
“Haka kuma sun yi garkuwa da mutum uku – mata biyu da yaro ɗaya.”
Mambobin Community Watch Corps (CWC) sun yi musayar wuta da ƴan bindigar tare da kai waɗanda suka ji rauni asibitoci a Funtua da Katsina, sai dai daga baya sun faɗa wa tarkon ƴan bindigar.
“An kashe jami’an tsaro biyu, an jikkata wasu takwas, an ƙone musu mota ɗaya,” in ji wani da ba a bayyana sunansa ba.
Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ya tabbatar da adadin waɗanda suka rasu, ya kuma yaba da jajircewar jami’an sa kan, yana mai cewa, “Jarumtar su ta hana mummunan abin da ya fi haka faruwa.”
Lamarin ya sake haskaka yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar ƙauyukan Kudancin Katsina duk da ƙoƙarin jami’an tsaro a yankin.