Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnatin tarayya sun sake neman a duba mafi ƙarancin albashi na ƙasa, suna masu cewa naira 70,000 yanzu bata dace da halin tattalin arziƙin ƙasar ba.
Wannan kiran na zuwa ne bayan wasu jihohi da dama sun ɗaga mafi ƙarancin albashinsu sama da naira 70,000 domin magance tsadar rayuwa, ciki har da jihar Imo wadda ta kai mafi ƙarancin albashin ma’aikata naira 104,000 tun 27 ga Agusta, 2025.
Idan ba a manta ba, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sabunta mafi ƙarancin albashi a watan Yuli 2024, inda aka ɗaga mafi ƙarancin daga ₦30,000 zuwa ₦70,000.
Benson Upah, Sakataren wucin gadi na NLC, ya shaida wa NAN cewa hauhawar farashi ta lalata kimar ₦70,000, ta bar ma’aikata da matsalar biyan buƙatun yau da kullum.
“Gaskiya ita ce ₦70,000 ba zata iya ɗaukar nauyin rayuwa ba a wannan yanayi. Idan gwamnati ba ta yi gaggawa ba, matsalar rayuwa za ta ƙara muni,” in ji shi.
Shi ma shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati, Shehu Mohammed, ya yaba wa gwamnonin jihohi da suka ɗaga albashin ma’aikatansu.
“Tun farko mun buƙaci albashin da zai inganta rayuwar ma’aikaci, muka gabatar da ₦250,000 a matsayin abin da ya dace,” in ji shi, yana mai cewa “idan aka cire kuɗin lantarki da sufuri, abin da ya rage ba zai kai ma’aikaci kwana goma ba.”
Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka yi hira da NAN sun bayyana cewa da wuya a ci gaba da iya rayuwa da albashin yanzu.
Kemi George ta ce, “Lokacin da na biya kuɗin mota da sayen abinci, babu abin da ya rage. Hayar gida da kuɗin makaranta sun gagare mu biya.”
Wasu ma’aikatan, ciki har da Obi Chimaobi da Bola Akingbade, sun yi kira da gwamnati ta gaggauta ƙara kuɗi, suna masu cewa albashi mai kyau zai ƙara inganta aiki, ya rage cin hanci a gwamnati, ya kuma yaƙi talauci.