Ƙungiyar Ɗaliban da Suka Kammala Karatu ta Jami’ar Bayero Kano, BUK (BUKAA) ta gudanar da taron shekara-shekara karo na 35 a ranar Asabar, 6 ga Satumba, 2025, inda manyan tsofaffin ɗalibai daga dukkan shiyyoyi shida na Najeriya suka hallara domin tunawa, haɗa kai, da sabunta ƙuduri kan ci gaban tsohuwar makarantarsu.
Wakilinmu, Hussain Isah ya rawaito cewa, Shugaban Jami’ar, Farfesa Haruna Musa, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan ajin shekarar 1991, ya yaba da yadda shugabancin BUKAA ke ci gaba da tabbatar da muhimmancin ƙungiyar, tare da yin kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da tsofaffin dalibanta.
“Jami’ar Bayero na samun ci gaba sosai, a yanzu muna matsayi na 6 cikin manyan jami’o’in Najeriya, na 4 cikin jami’o’in gwamnati, kuma na 1 a fagen tsaro a duniya. Tare da ingantaccen shugabanci, haɗin kai, da ƙarin kuɗaɗe, za mu ɗaukaka jami’ar zuwa mafi girma,” in ji shi.
Shugaban Majalisar Gudanarwar jami’ar, Air Vice Marshal Saddik Isma’ila Kaita (mai ritaya), ya shawarci ƙungiyar da ta sa rana ta musamman ta tsoffin ɗalibai domin ƙarfafa zumunci, musayar ra’ayoyi da kuma taimakawa ɗaliban da ke karatu su fahimci muhimmancin irin wannan alaƙa.
A jawabin babban baƙo mai jawabi, Ambasada Shuaibu A. Ahmed, tsohon Babban Sakataren Hukumar Rahoton Kuɗi ta Ƙasa, wanda Alhaji Ali Madugu na Kamfanin Dala Foods ya wakilta, ya ce tsarin shugabanci mai nagarta na da matuƙar muhimmanci ga ƙungiyoyin da ba riba, saboda riƙo gaskiya da fitar da bayyanai na ƙara ƙarfin amincewa, ɗorewa, da tasiri ga al’umma.
Sanata Ibrahim Shekarau, wanda shi ne ya shugabanci taron, ya yaba da cigaban ƙungiyar tare da yin kira da a tabbatar da haɗa kowa da kowa.
“Har yanzu akwai ƙalubale a gaba. Dole ne mu tabbatar dukkan tsofaffin ɗalibai suna cikin shiri tare da haɗin kai,” in ji shi.
A yayin zaman gudanarwa, mambobi sun amince da rahoton samu da kashe kuɗaɗen ƙungiyar, suka yi wa shugabancin BUKAA ƙarin ƙwarin gwiwa, tare da yin alƙawarin ci gaba da tallafawa.
Haka kuma, a wani muhimmin mataki na tarihi, BUKAA ta ƙaddamar da nata shafin yanar gizo na musamman – irinsa na farko.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Shuaibu Idris, ya bayyana wannan dandalin a matsayin sabon babi da zai sauya tsarin hulɗar tsofaffin ɗalibai.
“Ko ka kammala a 1980 ko a 2020, wannan shafin zai sauƙaƙa haɗuwa, sadarwa da bayar da tallafi,” in ji shi.
Ya kuma bayyana wasu ayyukan da ƙungiyar ke gudanarwa, ciki har da samar da ruwa a sabon sashen jami’ar (New Site), gyaran banɗakunan ɗalibai, da kafa babban asusun tallafi don ci gaban BUK.
A farko, a jawabin maraba, Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa an jinkirta taron na bana daga farkon shekara zuwa ƙarshen shekara saboda wasu dalilai, tare da tabbatar da cewa tarurruka masu zuwa za su koma farkon shekara ko tsakiyar shekara.
Mataimakin Shugaba na Farko, Aare Akinkunmi Akinyemi, ya yi godiya ga duk wanda ya ba da gudummawa wajen nasarar gudanar da taron shekara-shekarar karo na 35.