Ƙungiyar Likitocin Asibitocin Gwamnati ta Ƙasa (NARD) za ta gudanar da taron Majalisar Zartarwarta ta Ƙasa (NEC) a yau Laraba domin yanke shawara da ɗaukar mataki na gaba kan wa’adin kwanaki 10 da ta bai wa gwamnatin tarayya.
Ƙungiyar ta bayar da wa’adin kwanaki goma ga hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki, inda ta gargaɗi cewa za ta shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya idan ba a biya buƙatunta ba kafin wa’adin ya ƙare.
Wannan barazana ta zo ne a daidai lokacin da tsarin kiwon lafiyar gwamnati ke fuskantar ƙalubalai masu tsanani – ƙarancin likitoci, lalatattun cibiyoyin lafiya da cunkoson marasa lafiya a manyan asibitoci.
Wakilinmu ya tattaro daga takardar sanarwar da NARD ta fitar a ranar 1 ga Satumba, 2025, wacce shugabanta, Dr. Tope Osundara; Sakatare Janar, Dr. Oluwasola Odunbaku; da Sakataren Yaɗa Labarai, Dr. Omoha Amobi, suka sanya wa hannu, cewa ƙungiyar na neman a biya bashin kuɗaɗen horon likitocin da ke karatun samun ƙwarewa (MRTF) na 2025, a biya ariyas na watanni biyar na ƙarin albashin CONMESS kashi 25–35, da sauran bashin albashi da aka daɗe ba a biya ba.
Haka kuma ƙungiyar ta nemi a biya bashin kuɗin kayan aiki na shekarar 2024, a fitar da kuɗin ƙarin albashi ga ƙwararru ba tare da jinkiri ba, da kuma a dawo da sahalewar takardun ƙwarewar likitoci na kungiyar West African College of Physicians.
Har ila yau, ƙungiyar ta buƙaci Kwalejin Koyar da Likitanci ta Ƙasa ta bai wa duk waɗanda suka cancanta takardar shaidar zama membobinta, ta aiwatar da sabon tsarin albashi na 2024 (CONMESS), ta warware batun walwalar likitocin Kaduna, da kuma magance halin likitocin LAUTECH, Ogbomoso.
Da yake magana da jaridar The PUNCH jiya Talata, Dr. Osundara ya bayyana cewa, “Za mu gudanar da taron NEC gobe (yau kenan), kuma sakamakon taron zai fayyace matakinmu na gaba. A taron, za mu tantance ko gwamnati ta samar da wani gagarumin ci gaba wajen warware buƙatunmu. Idan akwai amsa mai kyau, hakan zai jagoranci shawarar da NEC za ta yanke, amma in ba haka ba, za mu ɗauki tsatstsauran mataki, ciki har da yiwuwar shiga yajin aiki.”
Haka ma, Mataimakin Shugaban NARD na Ƙasa, Dr. Tajudeen Abdulrauf, ya tabbatar da cewa NEC za ta sake taro a yau domin duba matsayin gwamnati kan buƙatun.
“Sakamakon taron zai dogara ne da amsar gwamnati. Idan ba a magance buƙatun ba, ba za mu iya tabbatar da zaman lafiya a fannin lafiya ba, kuma yajin aiki na iya zama dole. Kada a manta, mun bayar da wa’adin makonni uku a watan Yuli, muka kuma tsawaita shi domin tattaunawa, amma har yanzu ba a yi komai ba. Lokacin da muka zauna gobe (yau kenan), za mu tantance amsar gwamnati, mu yanke hukunci kan mataki na gaba,” in ji shi.
Masana sun yi gargaɗin cewa sabon yajin aikin zai iya lalata tsarin kiwon lafiya na gwamnati, ya tilasta marasa lafiya su koma asibitoci masu zaman kansu masu tsada, ya kuma ƙara taɓarɓarewar lafiyar jama’a a faɗin ƙasa.