Ƙididdigar INEC ta fitar da yawan sabuwar rijistar masu zaɓe adadin da ya wuce miliyan 4.4, yankin Kudu maso Gabas na kurar baya

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce sama da ƴan Najeriya miliyan 4.4 ne suka yi rajistar zaɓe ta yanar gizo cikin makonni huɗu kacal da fara aikin a ranar 18 ga Agusta 2025.

A wata sanarwa da Kwamishinan hukumar kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Sam Olumekun, ya fitar ranar Litinin, an bayyana cewa zuwa Lahadi 14 ga Satumba 2025, an yi rijistar masu kaɗa ƙuri’a 4,445,505 ta yanar gizo.

Sanarwar ta ce, “Daga cikin wannan adadi, 2,141,294 (kashi 48.17%) maza ne, yayin da mata suka kai 2,304,211 (kashi 51.83%).

Mafi rinjaye daga cikin masu rajistar, wato 2,924,643 (kashi 65.79%), matasa ne ƴan tsakanin shekaru 18 zuwa 34, yayin da ɗalibai suka kai 1,112,344 (kashi 25.02%).”

Wakilinmu ya fahimta daga bayanan INEC cewa, Jihar Osun ce ta ja ragamar rajistar da 552,045, yayin da Legas ta bi ta da 488,523.

A Arewa maso Gabas kuwa, Borno ta yi fice da rajistar 439,426.”

Ogun ta samu 396,799, Kebbi ta kai 287,059, Kaduna 240,357, Kogi 218,397, yayin da Babban Birnin Tarayya (FCT) ya samu 213,732.

Yobe ta biyo baya da 212,840, sai Oyo da 181,518.

A Arewa maso Yamma, Kano ta samu 113,547, Jigawa 93,292, da Kwara daga Arewa ta Tsakiya mai 93,106.

Daga yankin Kudu, Delta ta samu 81,353, Ekiti 85,209, sai Sokoto 75,761, da Niger 72,947 daga Arewa.

Bauchi da Imo sun samu 63,535 da 62,237 bi da bi, yayin da Katsina ta yi rajistar 61,143.

A ƙasan jerin yawan masu rijistar, Ebonyi tana da 4,024, Abia 3,532, sai Enugu da ta fi kowa ƙasa da rijista 1,839.

Wannan bambancin ya haifar da damuwa a Arewa, inda shugabannin al’umma, malamai da ƙungiyoyin farar hula suka fara ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a domin ƙara yawan masu rajista, musamman a ƙauyuka.

Sanarwar ta INEC ta kuma bayyana cewa, adadin rijistar da aka kammala – wanda ya haɗa rajistar kan yanar gizo da ta kai tsaye – ya kai 509,929 zuwa ranar 12 ga Satumba.

Daga ciki, 229,758 maza ne, yayin da mata suka kai 280,171.

Mafiya rinjaye matasa ne (378,132), ciki har da ɗalibai 196,529.

INEC ta ƙara da cewa, rajistar kan yanar gizo a FCT ta ƙare ranar Litinin, 15 ga Satumba 2025.

Za a ci gaba da yin rajista ta kai tsaye na tsawon makonni biyu a cibiyoyi da aka ware, kafin a baza cibiyoyin zuwa dukkan ƙananan wurare 62 daga 29 ga Satumba zuwa 8 ga Oktoba.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

INECRijistaZabe
Comments (0)
Add Comment