Ƙasashen da suka amince da Ƙasar Falasdinu da waɗanda ba su amince ba, da abin da hakan ke nufi

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

A ranar Lahadi, ƙasashe kamar Birtaniya, Ostiraliya, Kanada da Portugal sun bayyana amincewa da ƙasar Falasdinu, shekaru kusan biyu bayan fara yaƙin Gaza, yayin da wasu ƙasashe ciki har da Faransa da Belgium ke shirin bin sahu a Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilinmu ya fahimci cewa, ƙasar Falasdinu ta bayyana kanta a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta a 1988, amma har yanzu Isra’ila na riƙe da Yammacin Kogin Jordan, yayin da Gaza ke cikin farmakin ruguza gine-ginenta.

Bisa ga ƙididdigar AFP, aƙalla ƙasashe 145 daga cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 sun amince da ƙasar Falasdinu.

Wannan ya haɗa da Birtaniya da Kanada, waɗanda suka kasance ƙasashen G7 na farko da suka yi hakan, tare da Ostiraliya da Portugal.

Faransa, Belgium, Luxembourg da Malta suna shirin bayyana amincewarsu a taron ƙolin Majalisar Dinkin Duniya game da samar da mafita mai ƙasa biyu tattaunawar da Faransa da Saudiyya ke jagoranta a New York ranar Litinin.

Tun daga 1988, Algeria ta kasance ƙasar farko da ta amince da Falasdinu, sa’annan wasu ƙasashe da dama suka bi sahu a cikin ƴan watanni.

Yayin da harin Hamas a Isra’ila a 7 ga Oktoba, 2023 ya haifar da sabon ƙarfin samun amincewa daga ƙasashe 13.

Amma wasu ƙasashe, ciki har da Isra’ila, Amurka, Japan, Koriya ta Kudu da Singapore ba sa amince da ƙasar ba.

A Turai, ƙasashen sun kasa cimma ra’ayi ɗaya, yayin da yaƙin Gaza ya sauya wasu daga cikin matsayin ƙasashen kamar Birtaniya da Portugal.

Masana sun bayyana cewa amincewa da ƙasar Falasdinu yana da nauyi na siyasa, amma ba ya nufin ƙasar ta kasance wadda ta dace da doka ba.

Romain Le Boeuf, ƙwararre a shari’ar ƙasa da ƙasa, ya ce, “Amincewa ba yana nufin ƙasa ta halatta ba, kuma rashin amincewa ba ya hana ƙasar kasancewa.”

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

BirtaniyaFalasdinuGaza
Comments (0)
Add Comment