Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Ƙaramar Hukumar Hadejia a jihar Jigawa ta fara aikin gina rami mai tsawon kilomita uku domin bai wa ruwa hanya daga wani tafki zuwa Kogin Hadejia, a wani yunƙuri na magance matsalar ambaliya da ke addabar al’ummar yankin.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Malam Muhammad Talaki, ya miƙawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Dutse ranar Juma’a.
Talaki ya bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Ahmed Abba-Ari, ne ya ƙaddamar da aikin a Hadejia, wanda ya zai laƙume kimanin naira miliyan 60.
A cewarsa, Abba-Ari ya ce, “Wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin majalisar wajen samar da mafita ta dindindin ga ambaliyar da ke addabar al’ummomin da ke kewaye da tafkin da aka fi sani da Jaribola.”
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi ƙarin bayani cewa, ambaliyar da ake samu duk shekara na lalata gonaki, kasuwanni, da raba mutane da gidajensu, tare da rusa hanyoyin samun abin dogaro na al’ummar yankin.
Ya jaddada ƙudirin majalisar wajen samo hanyar da za ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Gina ramin zai rage tsananin illar ambaliyar da ake fuskanta a kowacce kakar damina, kuma zai inganta tsarin sarrafa ruwa a wannan yanki,” in ji shi.
Shi ma shugaban sashen ayyuka na ƙaramar hukumar, Alhaji Muhammad Ubale, ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa kamfanin da aka damƙawa aikin zai kammala shi bisa yarjejeniyar da aka cimma, tare da samar da duk wasu kayayyakin da ake buƙata.
Rahotannin majiyoyi sun nuna cewa ambaliya ta daɗe tana zama babbar matsala a Jigawa, inda ruwan sama da kwararar koguna ke raba dubban mazauna da muhallansu a kowace shekara.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook